1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 5 sun mutu sakamakon fada a birnin Mogadishu.

December 23, 2007
https://p.dw.com/p/CfY5

Akalla mutane 5 sun rasa rayukansu, a yayin da wasu takwas sukaji raunuka a wata arangama tsakannin dakarun ƙungiyoyin kotunan Islama da sojojin Somalia masu samun goyan bayan dakarun Habasha. Tun bayan da sojojin gwamnati tare da hadin-gwiwar Habasha suka kifar da gwamnatinsu a farkon wannan shekara, dakarun ƙungiyoyin kotunan Islama, suke ta kai harin boma-bomai kan babban birnin Mogadishu. Majalisar Dunkin Duniya ta yi kashadi game da irin bala’in da zai iya fuskantar al’uman ƙasar, sakamakon rikicin da ta ce ya yi sanadiyar tagayyarar duban jama’a.