1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 48 suka rasa rayukansu a Assam,India

Mutane 48 ne suka rasa rayukansu a hare hare daban daban yau a jihar Assam dake yankin arewa maso gabashin kasar India,wanda aka danganta da kungiyar yan tawaye da ake kira United Liberation Front of Assam da akatawa.Kawo yanzu dai babu wata kungiya data dauki alhakin kai wadannan jerin hare haren boma boma bomai wanda ya fara daga jiya.8 daga cikin jerin hare haren 10,sun auku ne garin Burma dake kann iyakr kasar ta India,ayayinda ajiya ne kuma wasu boma bomai suka tarwatse a babbar hanyar jiragen kasa dake wannan kasa.Daga shekarata 1979 Kawo yanzu dai an kiyasta cewa mutane dubu 20 suka rasa rayukansu a jihar ta Assam dake India.