Mutane 40 sun rasu a hadarin fashewar kayan wasan wuta a Pakistan | Labarai | DW | 11.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 40 sun rasu a hadarin fashewar kayan wasan wuta a Pakistan

Akalla mutane 40 dake dawowa daga wajen bikin aure suka rasu lokacin da kayakin wasan wuta da suke dauke da su suka fashe a cikin wata safa da suke ciki. Wannan hadarin ya auku ne a birnin Lahore dake gabashin kasar Pakistan. Rahotanni sun ce wani daga cikin mahalarta bukin ya jefa wani abin wasan wuta amma sai yayi bindiga a karkashin tankin safar kuma cikin kiftawa da bismillah sai sauran kayan wasan wutar dake cikin safar suka kama da wuta, abin da yayi sanadiya mutuwar akalla mutum 40 sannan 12 suka ji raunuka. Babban jami´in ´yan sanda a birnin na Lahore ya ce an gano dukkan gawawwakin mutanen da suka kone.