1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 33 sun mutu sakamakon rushewar gada akan jirgin kasa a India

Sakamakon rushewan gada da safiyar yau akan wani jirgin pasinja a gabashin India,rahotanni daga kasar na nuni dacewa mutane 33 kawo yanzu suka rasa rayukansu.Ya dauki jamian agaji saoi da dama kafin a cimma cirre karafa da manyan duwatsun rusasshiyar gadar daga kann jirgin daya ritsa da wannan hatsari da safiyar yau.Hadarin dai ya auku ne a kusa da tashar jiragen kasar dake garin Bhagulpar,a jihar Bihar dake gabashin India.Hadarin na yau ya auku ne adaidai lokacin da ake kokarin rusa gadar,da aka gina shekaru 140 da suka gabata.