Mutane 30 sun mutu cikin wani hari a Kaboul | Labarai | DW | 19.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 30 sun mutu cikin wani hari a Kaboul

A Afganistan mutane akalla 30 sun hallaka a yayin da wasu 320 suka ji rauni a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wata cibiyar jami'a tsaro ta tsakiyar birnin Kaboul a wannan Talata.

A Afganistan mutane akalla 30 sun hallaka a yayin da wasu 320 suka ji rauni a cikin wani harin kunar bakin wake da harbe-harben kan mai uwa da wabi da aka kai a wata cibiyar jami'a tsaro ta tsakiyar birnin Kaboul a wannan Talata.

Komishinan 'yan sandar birnin na Kaboul Abdul Rahman Rahimi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na reuters cewa mutanen da harin wanda aka kai da wata mota da aka dana wa bam ya rutsa da su sun hada da jami'an tsaro da kuma fararan hula.

Tuni dai Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan hari a cibiyar horas da jami'an tsaro masu tsaron lafiyar ministoci da manyan jami'an gwamnati. Shugaban kasar ta Afganistan Ashraf Ghani ya yi tir da Allah wadai da kai wannan hari.