1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 29 su mutu a Japan a girgizar ƙasa

Abdourahamane HassaneApril 16, 2016

Wata girgiza ƙasa mai karfin gaske da maki bakwai da digo uku a mauni Richter ta sake afkuwa a Kudu maso Yammaci Japan a daren Jumma'a zuwa Asabar a tsibirin Kyushu.

https://p.dw.com/p/1IWtH
Japan Neustart Kernkraftwerk Sendai
Hoto: Reuters/I. Kato

Girgizar wacce ta haddasa zabtarewar ƙasa da kuma gobara tare da katse hanyoyin sadarwa da na lantarki ta kashe mutane guda 19, kuma tun farko a ranar Alhamis da ta wuce girigza ta halaka mutane tara a yankin.

A halin da ake ciki gwamnatin Japan ta baza sojoji dubu 40 domin yin aikin ceto, kuma tuni da aka kwashe wasu jama'ar kamar mutun dubu 30 daga inda lamarin ya faru.

Firaministan Japan Shinzo Abe wanda ya kai ziyarar gani da ido ya sha alwashin taimakawa jama'ar.Ya ce:'' Muna ƙara gudanar da bincike domin tantance ta'adin da girgizar ƙasar ta haddasa don kawo daukin da ya dace ga jama'ar da lama'rin ya shafa.