Mutane 24 sun rasa rayuka a taron yaƙin neman zaɓe a Yamal | Labarai | DW | 12.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 24 sun rasa rayuka a taron yaƙin neman zaɓe a Yamal

A ƙalla mutane 24 su ka rasa rayuka, sannan da dama su ka ji mummunan rauka, a ƙasar Yamal, a yayin taron gangamin siyasa, bisa jagorancin shugaban ƙasa Ali Abdallah Saleh.

Wannan haɗari ya abku a cikin tustastoniya, a filin ƙwalon Ibb, da ke tazara kilomita 180, a kudancin Sannaa babban birnin ƙasar.

Fiye da mutane dubu ɗari,su ka taru a wannan filin ƙwalon domin sauraran jawabin yaƙin neman zaɓe, da shugaban ƙasar ya gabatar.

Ranar 20 ga watan da mu ke ciki ne, za shirya zaɓen shugaban ƙasa da na yan majaliosun dokoki ,a Yamal.

Saidai tunni, manazarta sun tabbatar da cewa, shugaba mai ci yanzu, wanda ke kan karagar mulki, tun shekara ta 1978 zai yi tazarce, tun zagaye na farko.

Baki ɗaya yan takara 4 ne, su ka bayyana shawar maye kujerar shugabancin ƙasar da ke matsayin ɗaya, daga ƙasashe mafi talauci a dunia.