Mutane 20 sun rasu a harin Kamaru
July 26, 2015Aƙalla mutane 20 ne a ke saran sun mutu bayan wani farmakin bam a wata mashaya daren Asabar a birnin Maroua da ke Arewacin Kamaru kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.Wannan farmaki dai na zama na biyu a yankin bayan hari da aka kai a ranar Laraba da yayi sanadin kisan mutane 13 a wasu tagwayen hare-haren bama-bamai da aka yi amfani da wasu ƙananan yara 'yan mata wajen kai shi.
A cewar wani soja da ke aikin yaƙi da mayaƙan Boko Haram da bai so a bayyana sunansa ba ya ce da misalin karfe 9:30 ne agogon ƙasar takwas da rabi agogon GMT aka kai wannan farmaki . A cewar majiyar jami'an gwamnati akwai mutane da dama da suka sami raunika a wannan hari.Wasu da suka ga yadda lamarin ya afku a lardin na Ponre sun bayyana cewar maharin ya jefa bama-baman ne a mashayar sannan ya ruga a guje lokacin da wadanda ba su sami raunika ba suka bi shi sai ya riƙa jefa musu makaman gurneti abin da ya sanya ya gudu.
A ranar Laraba ma a tagwayen hare-haren da aka kai babbar kasuwa da yankin da ke kusa mutane 13 ne suka rasu.