1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 19 sun hallaka a Masar

February 26, 2013

Fashewar wani balan-balan wanda ke yawo da masu yawon bude ido a Masar, ya kama wuta ya fashe, mutane 2 kadai suka yi rai daga cikin 21

https://p.dw.com/p/17m3Z
FILES - In this 06 April 2009 file photo tourists in hot air balloons fly over Luxor's famed West Bank Temples and the Valley of the Kings in Egypt. EPA/MIKE NELSON (zu dpa "Heißluftballon mit Touristen stürzt in Ägypten ab" vom 26.02.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani babban balan-balan wanda mutane kan shiga dan ganin birane ta sama idan sun je yawon buɗe ido ya faɗi a birnin Luxor na ƙasar Masar inda ya kai ga hallakar mutane 19. Wakilin masu kula da tsaron irin wannan shaƙatawar ya ce mutanen da suka rasun sun fito ƙasashen da suka haɗa da Burtaniya, da Faransa da Japan da China. Mutane 21 ne ke cikin wannan balan-balan wanda ya wuce da su ta wani gefen birnin Kurna, suna tafe a bisan meta 300 daga doron ƙasa, kafin wuta ta kama ta kuma kai ga fashewar balan-balan din.

Mutane biyu suka yi rai a wannan hatsari, a cikinsu da matuƙin balan-balan din, kuma a yanzu haka yana ƙarbar magunguna a asibiti. Birnin Luxor yana kusa da kogin Nile kuma yana da manyan-manyan wuraren ibada tun na zamanin Firauna waɗanda ke zaman ɗaya daga cikin wuraren da maziyarta suka fi sha'awar gani, kuma gewaya wannan wuri cikin irin wannan bala-balan yayi suna sosai, to sai dai yanzu an fara samun haɗarruruka wajen yinsa.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu