Mutane 17 suka mutu a gobarar Landan
June 15, 2017Talla
Shugaban jami'an aikin kwana-kwana na Landan Dany Cotton ya ce da wuya a samu wadanda ke da sauran shan ruwa a gaba a cikin yanayin da wutar take kara ruruwa ga kuma tsananin zafi. Wasu kafofin yada labarai sun ambato gomai na iyalai da suka bace wadanda har ya zuwa yanzu ba a ji duriyar su ba. Ko da shi ke ya zuwa yanzu ba san dalilan tashin gobarar ba, amma dai ,jama'ar da ke zaune a soron benen na yn korafin a game da rashin tsari wajen tafiyar da ayyuka samar da lantarki a benen.