1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 16 sun rasa ransu a Iraki

Zulaiha Abubakar
April 12, 2018

A kalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu a yayin da suke tsaka da gabatar da jana'izar wasu mayakan kasar Iraki wadanda 'yan kungiyar ta'adda ta IS suka hallaka.

https://p.dw.com/p/2vxIR
Symbolbild Islamischer Staat Propaganda Video Still
Hoto: picture-alliance/abaca

Salaheddin Shaalan magajin garin Sharqat, ya shaidawa manema labarai cewa  mutane 14 na kwance a asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon harin da aka kai a makabartar. Kasar ta Iraki dai ta jima tana fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyar mayakan na IS da suka addabi kasashen Irakin da Siriya, kana suke neman zama annoba a duniya baki daya.