Mutane 15 sun rasu a sakamakon wata iska mai karfi da ta ratsa Amirka | Labarai | DW | 06.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 15 sun rasu a sakamakon wata iska mai karfi da ta ratsa Amirka

Akalla mutane 15 sun rasu sannan wasu daruruwa sun samu raunuka sakamakon wata isaka mai karfin gaske da ta ratsa kudancin jihar Indiana da Kentucky dake kasar Amirka da sanyin safiyar yau lahadi. Iskar dai ta zo ne a ba zata ba tare da wani gargadi ba da misalin karfe biyun dare a daidai lokacin da mutane ke barci. Hukumomi sun ce an ji karar jiniya ta gargadi kimanin mintoci 10 gabanin iskar ta ratsa wandannan yankuna. Iskar ta haddasa mummunar barna yayin da dubun dubatan mutane kuma ke zaune a gidaje yanzu haka ba wutar lantarki.