Mutane 14 sun halaka a Iraqi | Labarai | DW | 27.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 14 sun halaka a Iraqi

Wasu mutane 14 a iraqi sun rasa rayukan su wasu kuma 10 sun jikkata.

Hakan kuwa ya biyo bayan tashin wani bom ne da nan kunar bakin wake yayi, a cikin wata mota kirar bus da akace an sace tane.

A cewar rahotanni bom din ya tashi ne a cikin motar, a tsakayar birnin Ramadi dake kasar ta Iraqi.