1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 13 sun mutu a wani hari a kudu maso yammacin Pakistan

Akalla mutane 13 aka halaka a wani harin bam da aka kai kan wata safa a lardin Baluchistan dake kudu maso yammacin kasar Pakistan. Jami´ai sun ce akalla mutane 20 sun samu ranuka a fashewar bam din wanda ya auku lokacin da motar safa din take kan hanya daga hedkwatar lardin na Baluchistan wato Quetta zuwa birnin Lahore. ´Yan sanda suka ce da alama an boye bam din ne a cikin wata jakka wadda aka ajiye ta karkashin kujerar mota kuma aka ta da ita da na´urar sarrafa abu daga nesa. Baluchistan yankin da ya fi samarwa Pakistan iskar gas, ya kasance wani dandalin tashe tashen hankula tsakanin ´yan tawaye da dakarun tsaro. Kawo yanzu ba wanda yayi ikirarin kai harin.