1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

mutane 12 suka mutu a sabon rikici a somalia

Akalla mutane 12 suka rasa rayukansu yau a Somalia,kana wasu 11 suka jikkata,lokacin da yansanda kasar sukayi arangama da wasu mutane dauke da bindigogi a filin saukan jiragen garin Baidoa dake zama matsagunnin gwamnatin rikon kwarya.Wannan fada dai ya barke ne adaidai lokacin da,wakilan gwamnatin rikon kwaryan kasar ke ganawa dana kungiyoyin kotunan musulmi a kasar Sudan.Rahotanni daga Baidoan dai na nuni dacewa,yansandan sun shiga filin saukan jiragen saman yankin ne da nufin koran mayakan da suka mamaye shi,kuma ke karban kudaden haraji na tilas,bayan an kore su a matsayin jamian tsaro a filin jirgin.Kakakin gwamnatin riko na somalia,Abdirahman Mohammed Nur Dinari,yace an umurci yansanda a halin yanzu dasu kula da harkokin filin saukan jiragen saman na Baidoa,ayayinda ake cigaba da kwashe wadanda suka jikkata sakamakon wannan arangama.

 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5b
 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5b