Mutane 103 suka rasu a hadarin jirgin sama a Nijeriya | Labarai | DW | 11.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 103 suka rasu a hadarin jirgin sama a Nijeriya

Akalla mutane 103 ciki har da ´yaran makaranta da dama suka rasu sakamakon hadarin wani jirgin saman fasinja a birnin Fatakwal dake kudancin tarayyar Nijeriya. Kafofin yada labarun kasar dai sun ce jirgin saman mallakin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Sosoliso da ya taso daga birnin Abuja, ya goce hanya ne kuma ya kama da wuta lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin saman Fatakwal mai arzikin man fetir a kudancin tarayyar ta Nijeriya. Rahotanni sun ce mutane 7 sun tsira da rayukansu a wannan hadarin. Ko da yake kawo yanzu ba´a san musabbabin aukuwar hadarin ba, amma rahotanni sun ce ana hadari a wannan lokaci. Wannan hadarin dai ya auku ne kasa da wata biyu bayan hadarin wani jirgin saman fasinjan kamfanin Bellview a kusa da birnin Legas wanda ya halaka mutane sama da 100 dake cikin jirgin.