1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 10 sun mutu a lokaci zaɓen Philippines

May 10, 2010

Rikici da salwantar rayuka sun mamaye zaɓukan da ke gudana a ƙasar Philippines.

https://p.dw.com/p/NKTu
Hoto: AP

Tashe-tashen hankula na ci gaba da haifar da tsaiko a zaɓen shugaban ƙasa da kuma na 'yan majalisa da ke gudana a ƙasar Philippines. Aƙalla mutane goma ne aka tabbatar da cewa sun rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu sama da 20 suka ji rauni a fito na fito da masu kaɗa ƙuri'a ke yi da jami'an tsaro a yankin Zamboaga. Kafin ma a kammala yaƙin neman zaɓen, sai da rikice-rikicen suka haifar da salwantar rayukan mutane goma.

Sama da mutane miliyion 50 ake sa ran zasu kaɗa ƙuri'a, domin zaɓen wanda zai maye gurbin shugaɓar wannan ƙasa wato Gloria Arroyo. Daga cikin 'yan takara da ake tsamanin za su yi nasara a zaɓen, har da Senata Benigno Aquino, wato ɗa ga tsohon shugaban ƙasar ta Philippines Corazon Aquino.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Edita: Mohammad Awal