Mutane 10 sun jikata sakamakon rokokin da Hisbollah ta harba akan birnin Haifa | Labarai | DW | 21.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 10 sun jikata sakamakon rokokin da Hisbollah ta harba akan birnin Haifa

Wasu rokoki da Hisbollah ta harba daga Lebanon sun afkawa birnin Haifa dake arewacin Isra´ila inda suka raunata akalla mutane 10. Daya daga cikin rokoki ya fadi akan wani gida. An ji karar jiniya jim kadan gabanin rokokin su afakwa birnin na Haifa. Kawo yanzu Hisbollah ta harba rokoki fiye da 900 akan garuruwa da kayuka na Isra´ila wanda ya yi sandiyar mutuwar fararen hula 15. A kuma halin da ake ciki Isra´ila ta kaddamar da hare hare a gabashin Lebanon inda ta halaka fararen hula 3, amma masu aikin ceto sun ce yawan wadanda suka rasu ka iya zarta haka. A cikin wata sanarwa da ta bayar rundunar sojin Isra´ila ta ce ta fara hada kan wasu bataliyoyi na sojojinta dake zaman jiran ko-takwana don karfafa yawan dakarunta a arewacin kasar, wadanda kuma zasu iya kutsawa cikin Lebanon. An yi kira ga mazauna kudancin Libanon da su fice daga yankin kan iyakar ba tare da jinkiri ba. A dai halin ake ciki ministan tsaron Libanon Elias Al Murr ya ce rundunar soji zata kare kasar daga duk wani mamaye daga ketare.