Mutane 10 suka mutu sannan wasu 17 suka ji rauni sakamakon wani harin kunar bakin wake a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan…. | Labarai | DW | 08.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 10 suka mutu sannan wasu 17 suka ji rauni sakamakon wani harin kunar bakin wake a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan….

Wani dan kunar bakin wake a birnin Kabul yayi sanadiyar mutuwan mutane 10 kana ya jiwa wasu 17 rauni. Harin wanda aka kai wa jerin motocin Amurka ya auku ne kusa da ofishin jakadancin Amurka kuma sojojin Amurka biyu na cikin wadanda suka rasa rayukan su. Kawo yanzu dai babu wani tabbaci akann yawan mutanen da harin ya rutsa da su, amma wasu rahotanni sun nuna cewar mutane 16 ne suka gamu da ajalin su. An kai wannan harin dai dai lokacin da janar janar na kungiyar tsaro ta NATO ke zaman tattauna yiwuwar aika karin jami’an tsaro zuwa Afghanistan a kasar Poland. James Appathurai kakakin kungiyar tsaro ya hakikance cewar suna fuskantar yawan hare hare na ‘yan taliban a Afghanistan.