1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi matasa na taka rawa wajen inganta zamantakewa a Jamus

Mohammad Nasiru AwalMarch 2, 2007

Ana aiwatar da shirye shirye da dama don kyautata fahimtar juna tsakanin matasan musulmi da takwarorin su Jamusawa.

https://p.dw.com/p/BvSz
Musayar yawu da juna
Musayar yawu da junaHoto: picture-alliance/dpa

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi al´adu, addinai da zamantakewa a sassa daban daban na duniya.

A gun wani taro mai taken musulmi a matsayin ´yan kasa wanda jam´iyun CDU da kuma The Greens suka shirya a birnin Berlin, an tattauna akan rawar da musulmi ke takawa wajen fasalta tsarin zamantakewa a Jamus. Bugu da kari taron ya kuma yi magana akan aikace aikace da musulmi matasa ke yi don inganta zaman cude ni in cude ka tsakanin mabiya addinai da al´adu dabam-dabam a wannan kasa. Ayyukan wadannan matasa sun hada da shirya fina-finai musamman don kawad da gurguwar al´adar nan ta danganta addinin Islama da ayyukan tarzoma da take hakkin mata. To shirin na yau zai duba irin gundunmawar da matasan ke bayarwa ne da nufin fahimtar da jama´a musulmi da wadanda ba musulmi ba, baki da Jamusawa game da addinin Islama da al´adun musulmi baki daya. Masu sauraro MNA ke lale marhabin da sake saduwa da ku a cikin shirin.

1. O-Ton Atmo Gebetsruf:

Madalla. A cikin jawabinsa na bude taron daraktan gidauniyar Heinrich-Böll mai alaka da jam´iyar The Greens, Ralf Fücks ya bayyana batutuwan da aka sa a gaba.

1. O-Ton Ralf Fücks:

“Burin mu shi ne tallafawa wani shiri wanda zai sa miliyoyin musulmi su gane cewa su ma wani bangare ne na al´umar wannan kasa. A matsayin su na ´yan kasa, zasu iya ba da gagarumar gudunmawa a fannoni siyasa, zamantakewa da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar jama´a.”

Wannan shirin ya tanadi jawo hankalin musulmin ta yadda za´a inganta sajewarsu da al´umar Jamus. A dangane da haka babban sakataren gidauniyar Konrad Adenauer mai alaka da jam´iyar CDU, Wilhelm Staudacher ya jawo hankalin ne yana mai cewa yin haka ya shafi dukkan sassan biyu.

2. O-Ton Staudacher:

“Hakan na bukatar sauyin salon tunanin mu. Dole mu karbe su da hannu bibiyu. Amma su ma musulmin dole su san irin rawar da zasu taka don inganta zamantakewa tsakanin wannan al´uma.”

Mesut Lencper matashi dan asalin kasar Turkiya, da wasu matasa ´yan asalin kasashen Larabawa da takwarorinsu Jamusawa sun kafa wata kungiyar mai suna Kiezboom a unguwar Wedding dake Berlin don tallafawa matasa wajen inganta hazakar su a fannoni dabam dabam da suka hada da na wasanni motsa jiki kade-kade da wake wake. Hakazalika kungiyar na taimakawa matasa marasa aikin yi da wayar musu da kai don kauracewa gudanar da ayyuka irin na bata gari.

4. O-Ton Lencper:

“Abin sha´awa a nan dai shi ne sauya tunanin matasan daga ayyuka na tarzoma da tashe tashen zuwa ayyuka na gari. Yanzu haka muna samun hadin kai da makarantun nasare da malaman makarantun firamare. Hakan kuwa ya fara yin kyakkyawan tasiri a tsakanin matasa.”

Wani sashe na matasan ya dukufa ne wajen shirya jerin fina-finai masu taken matasa da musulmi a Jamus. Mohammad Reza dan asalin Iran na daga cikin masu shirya fina-finan na al´adu da addinin Islama.

1. O-Ton Reza:

“Musulmi ba mu da cikakken wakilci a fagen aikin jarida da sauran kafofin yada labaru. Kullum wasu ne ke shirya fina-finai ko ba da rahotanni a game da mu, amma mu kan mu ba ma yin haka. Wato ba ma iya gabatar da kan mu da kan mu, sai wasu dabam ke gabatar da mu.”

A dangane da haka ne Mohammad bai yi wata-wata ba wajen gabatar da kansa lokacin da ake neman matasa ga shirin na hada fim din musulmi a Jamus a bara. Wannna shirin wanda ma´aikatar kyautata jin dadin iyali, manya, mata da matasa ke daukar nauyinsa, shi ne irinsa na farko mafi girma a fadin tarayyar Jamus. Daraktan shirin Andreas von Hören ya bayyana manufar da suka a gaba yana mai cewa.

3. O-Ton von Hören:

“Ana shirya fina-finan ne domin baki matasa wadanda suka mance asalinsu, ko dai na addini ko kuma na al´ada. Muna kuma mayar da hankali ga matasan Jamusawa wadanda ke neman karin sani a game da al´adun bakin. Muna kuma kokarin kawad da fargabar da ´yan jarida ke yadawa musamman game da al´umar musulmi sai samar da kyakkyawar kafar tattaunawa da juna.”

Daura dan kwali ga matan musulmin na ci-gaba da zama abin saka ayar tambaya ko shin tauye hakkin mace ba ne ko kuma alama ce ta sanin addinin? A cikin wani fim da wasu ´yan makaranta a nan Jamus suka yi ya nunar a fili duk wata mai yin lullubi ko daura dan kwali dole sai da dauriya wajen jurewa irin kallon raini da kaskanci da ake mata akan titi. To amma Asma´a da Sumaya sun ce duk da haka ba zasu taba cire dan kwalinsu a bainar jama´a ba.

4. O-Ton Asmaa:

“Ina daura dan kwali ne saboda imani da addinin Islama, amma ba saboda matsin lamba ba, domin ai babu tilas ga addini. Idan na ga dama sai in cire shi, kuma iyaye na ba zasu iya tilasta min in daura dan kwali ba.”

Ita kuwa Sumaya cewa ta yi.

5. O-Ton Sumaya:

“Lalle ina iya cewa shigar da nake yi ta musulunci da rayuwa ta akan dokokin addinin tamkar wani cikakken ´yanci ne a gare ni.”

Dukkan sassan biyu wato Jamusawa da musulmin kan su ba sa mayar da hankali sosai wajen tattaunawa da juna. A cikin fim din ta akan daliban musulmi a Jamus, Ilham mai karatun fannin tarihi da al´adun Jamus ta yi fatan cewa maimakon a yi ta nuna bambamci kamata yayi a kara mayar da himma wajen sanin al´adun juna.

7. O-Ton Ilham:

“Wasu kan tambayeni game da rayuwa a cikin addinin Islama. Ina matukar farin ciki ga irin wadannan tambayoyi. To amma wasu tsokana ce kawai suke yi amma ba neman sani ba. To amma ba na damuwa da haka, domin ba dole ba ne kowa ya yi maraba da abin da nake so.”

Ita kuwa Clemence Delmas mai karatu a fannin kimiyar siyasa ta na mai ra´ayin cewa an samu canji a tattaunawar da sassan biyu ke yi.

7. O-Ton Delmas:

“Kana iya ganin raguwar bambamce-bambamce. Yanzu an fara fitowa fili ana magana game da matsalolin dake hana ruwa gudu. Mun kawad da bambamce bambamce da dama. Idan na kwatanta da shekaru 3 da suka gabata, to ina iya cewa an samu canji.”