1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi a yankuna daban-daban na duniya, na ci gaba da gudanad da zanga-zangar nuna adawa ga buga hotunan zanen siffanta annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a wasu jaridun kasashen Yamma.

February 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9A

A yankuna daban-daban na duniya, musulmi sun ci gaba da zanga-zangarsu yau litinin, ta nuna matukar tashin hankalinsu game da batancin da ake yi wa annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ta hanyar buga hotunan zanen siffanta shi da aka yi, a cikinsu kuwa har da wani zanen da ke siffanta shi kamar dan ta’adda. Rahotannin da muka samu sun ce, a kusan duk muhimman kasashen musulmi an yi zanga-zangar, daga Indonesiya har zuwa Zirin Gaza.

A Indonesiyan dai, rahotannin sun ce musulmi sun yi zanga-zangar ne a manyan biranen kasar guda 4, inda suka yi kira ga Denmark da ta nemi gafara, saboda wadannan hotunan zanen da aka fara bugawa a kasarta. A birnin Surabaya, har ila yau dai a kasar Indonesiyan, wani gungun musulmi ya yi arangama da `yan sanda, a gaban karamin ofishin jakadancin Denmark, inda jami’an tsaron suka yi ta harba bindiga a sama da kuma barkonon tsohuwa, don su tarwatsad da masu zanga-zangar. An dai kuma yi zanga-zangar a kasashen Indiya, da Thailand da kuma Afghanistan, inda rahotanni suka ce, mutum daya ya rasa ransa, sa’annan mutane biyu kuma suka ji rauni, yayin da masu zanga-zangar suka kara da `yan sanda a garin Mehtarlam, da ke gabashin kasar.

A nan Turai ma, rahotanni sun ce kusan mutane dubu 4 ne suka yi maci a birnin Brussels na kasar Belgium jiya lahadi, sa’annan kusan musulmi dubu daya kuma suka yi wata zanga-zangar ta hannunka mai sanda a birnin Paris, kasar Faransa, don nuna bacin ransu ga buga hotunan zanen a jaridun kasashen. Kazalika kuma, a birnin New York a can Amirka, daruruwan musulmi ne suka yi wani taron gangami a ofishin manzancin kasar Denmark a Majalisar dinkin Duniya, inda suka yi kira ga kasar da ta nemi gafara.