1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi a Jamus

September 5, 2006

Ministan kuda da manufofin cude-ni-in-cude-ka a Northrhine-Westfaliya ya bayyana goyan bayan koyar da darussan musulunci a makaratun Jamus

https://p.dw.com/p/BvTL
Armin Laschet
Armin LaschetHoto: dw-tv

Shi dai Armin Laschet shi ne wani minista daya kwal da aka nada domin kula da manufofin zaman cude-ni-in-cude-ka a duk fadin Jamus. Ministan, dan jam’iyyar Christian Democrats baya sako-sako da barazanar ta’addancin da ake fuskanta daga wasu tsirarun musulmi dake da ra’ayi na tsageranci. Amma a daya hannun ya sikankance cewar ba za a fid da kauna a game da makomar shawarwarin neman kusanta da fahimtar juna ba. A lokacin da yake bayani game da haka Armin Laschet cewa yayi:

“A ganina dai shawarwarin na tafiya akan wata kyakkyawar hanya madaidaiciya a nan kasar. Bugu da kari kuma hare-haren sha daya ga watan satumba ba ya da wata nasaba da manufofinmu na kyautata zaman-cude-ni-in-cude-ka. Domin kuwa su kansu Musulmin dake nan kasar sun kadu matuka ainun a game da wadannan hare-hare. Su kansu ma dai ai ba zasu iya tsira daga wani bom da zai yi bindiga a jiragen kasa ba. A saboda haka wajibi ne a rika banbantawa tsakanin musulmi tsiraru masu zazzafar ra’ayi na akida, wadanda wajibi ne a tinkaresu ta kowace fuska da kuma musulmi mafiya rinjaye dake nan kasar wadanda basu da wata alaka da hare-haren 11 ga watan satumba daidai da mabiya darikar katolika wadanda basu da wata nasaba da hare-haren kungiyar IRA a Irland ta Arewa.”

Laschet dai ya kara da bayani akan dangantaka mai zurfin dake akwai a fannoni na musayar al’adu tsakanin musulmi da kiristoci da kuma yahudawa a nan Jamus. To sai dai kuma abin takaici shi ne ita wannan dangantakar tana wanzuwa ne tsakanin magabata bata hada da sauran talakawan kasa ba. Wani abin da zai taimaka a samu kyakkyawan ci gaba a wannan bangaren kamar yadda Laschet ke gani shi ne shigar da darussan addinin musulunci a makarantun Jamus baki daya, a maimakon matakai na gwaji da ake dauka a wasu makarantun a wawware. Laschet ya kara da cewar:

“A halin yanzu haka an gabatar da wani mataki na hadin guiwa tsakanin mahukunta da limaman masallatai a garuruwan Köln da Duisburg domin zayyana wata nagartacciyar manhajar darussan addinin musulunci tare da ba da la’akari da daftarin tsarin mulkin kasa kuma malaman da za’a dauka domin ko yarwa tilas ne su kasance sun samu horo ne a nan Jamus. Idan har wannan shiri ya samu nasara ba shakka zai iya zama abin koyi ga sauran garuruwa da jihohin Jamus.