Musulmai sun fara azumin watan Ramadan na bana
June 6, 2016Talla
Galibin Musulmai a kasashen duniya sun fara azumin watan Ramadan da ya daga cikin muhimman rukunan addinin. A ranar Lahadi mahukunta a Saudiyya sun bayyana cewa sakamakon ganin jaririn watan Musulmai a kasar sun tashi da azumin a wannan Litinin.
Kuma akwai kasashe da dama na Musulmai da suka bayyana haka, ciki har da Najeriya. A karshen watan za a yi bukukuwa na Sallah.