Musharraf ya ce ba zai ɗage dokat ta ɓaci ba
November 17, 2007Talla
Muƙaddashin sakatariyar harkokin wajen Amirka John Nigroponte ya gana da shugaban Pakistan Pervez Musharraf inda yayi kira a gare shi da ya ɗage dokar ta ɓaci da ya kafa a farkon wannan wata. To sai shugaba Musharraf ya ƙi ɗage dokar yana mai cewa za a ɗage ta idan lamuran tsaro suka inganta a kasar. Ziyarar Nigroponte zuwa Pakistan ta zo ne kwana guda bayan yayi magana da shugabar ´yan adawa Benazir Bhutto ta wayar tarho, wadda a jiya juma´a aka sake ta daga daurin talala a gidanta dake birnin Lahore na gabashin ƙasar. Gwamnati a birnin Washington tana fatan farfaɗo da yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin Musharraf da Bhutto a wannan lokacin da ake kara nuna damuwa dangane da tabarbarewar al´amuran a Pakistan.