1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musharraf na kiran tattaunawa

October 10, 2010

A cikin wata hira da aka yi da shi tsofon shugaban ƙasar Pakistan ya ce a shiga shawarwari da 'yan tawaye

https://p.dw.com/p/PakO
Tsofon shugaban Pakistan Pervez MusharrafHoto: picture-alliance/ dpa

Tsofon Shugaban ƙasar Pakistan Pervez Musharraf ya yi gargaɗin cewa hanyar tattaunawa tsakannin 'yan tawye da gwamnatin ita kaɗai ce mafi a'a ala da za ta kawo kwanciyar hankali a ƙasar.

Musharaf wanda a yanzu haka yake zaman hijira a Ingila kana kuma yake da niyyar tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2013 , ya yi kakkausan suka ga gwamnatin Amirka dake zargin Pakistan da yin sakaci wajan yaƙi da masu ta da zaune tsayen.

Da yake magana da wani gidan talabijin na Amirka wato ABC ya ce zai koma gida kafin zaɓuɓɓukan da aka shirya gudanarwa nan gaba.

Tsofon shugaban na Pakistan ya dai yi marabus ne a shekara ta 2008 sakamakon matsin lambar da aka yi masa na tsige shi daga karagar mulki.

Mawallafi: Abdurrahman Hassane

Edita: Ahmad tijani Lawal