1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musharraf da Bhutto sun cimma yarjejeniyar yiwuwar raba iko

October 5, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9L

Gabanin zaben shugaban kasa da za´a gudanar a Pakistan gobe asabar, shugaba Pervez Musharraf da tsohuwar FM kasar Benazir Bhutto sun cimma yarjejeniya akan yiwuwar raba madafun iko. Ministan sufurin jiragen kasa kuma na hannun damar shugaba Musharraf Sheikh Rashid ya sanar da cewa gwamnati a birnin Islambad da jam´iyar Benazir Bhutto sun amince a kan wata yarjejeniyar hada kan kasa. Wannan yarjejeniyar dai ta tanadi yin afuwa ga ´yan siyasa da shugabanci kasar ta Pakistan daga shekarar 1988 zuwa 1999. Wato kenan an wanke sunan Bhutto daga zargin cin hanci da rashawa wanda dalinlinsa ya sa ta yi gudun hijira na tsawon shekaru 8 a ketare.