Musayar wuta a Gaza tsakanin ´ya´yan Hamas da na Fatah | Labarai | DW | 17.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musayar wuta a Gaza tsakanin ´ya´yan Hamas da na Fatah

Magoya bayan kungiyoyin Hamas da Fatah da ba sa ga maciji da juna sun yi mummunar musayar wuta a kewayen harabar fadar shugaban kasa da ke tsakiyar birnin Gaza. An yi amfani da manyan bindigogi masu sarrafa kansu da karar fashewar rokoki a yankin yayin da masu fafatawa da junan ke kara jan daga a saman gine gine da kuma kan tituna. Da Farko wasu ´yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin ministan harkokin waje na Hamas Mahmud al-Zahar sannan kuma sun kai farmaki kan wani sansanin horas da dakarun tsaro masu biyayya ga shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Tabarbarewar halin da ake ciki a yankin ta zo ne kwana guda bayan sanarwar da Abbas ya bayar game da kiran sabon zabe na gaba da wa´adi, wanda Hamas ta bayana da cewa wani juyin mulki ne.