MUSAYAR FURSUNONI TSAKANIN ISRA′ILA DA KUNGIYAR HIZBULLAH A KOLON | Siyasa | DW | 29.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MUSAYAR FURSUNONI TSAKANIN ISRA'ILA DA KUNGIYAR HIZBULLAH A KOLON


An dai dau matakai dalla-dalla, don ganin cewa musayar ta auku kamar yadda aka yarje kanta. Mintoci kadan bayan karfe bakwai na safiyar yau, kuma yayin da dusar kankara ke ta zubowa ne, wasu jiragen saman rundunar sojin Jamus da na rundunar mayakan saman Isra'ila, suka sauka a filin jirgin saman Kolon-Bonn. Tun da asuba ne dai jiragen suka taso daga biranen Beirut da Tel Aviv. Jirgin mayakan saman Isra'ilan na dauke ne da fursunoni fiye da 30 masu asali daga kasashen Larabawa daban-daban, wadanda tun shekaru da dama ne suke daure a kurkukun Isra'ila. Daya jirgin kuma, wato na rundunar sojin Bundeswehr ta nan Jamus, wanda shi ne ya taso daga Beirut, ya kawo gawawwakin wasu sojojin Isra'ila guda 3 ne, wadanda suka mutu a kudancin Lebanon tun shekaru 3 da suka wuce, tare kuma da wani dan kasuwan Isra'ilan, wanda kungiyar Hizbullahin ta cafke a birnin Beirut a cikin watan Oktoban shekara ta 2000. Kafin saukowar jiragen dai, dimbin yawan maneman labarai sun taru suna neman gano wa idanunsu yadda musayar za ta kasance. To sai dai, saboda tsauraran matakan tsaron da aka dauka, ba su sami sun kai kusa kusa da filin da jiragen suka sauko a kansa ba. Daga nesa ne dai wani rukunin masu daukar hoton talabijin ya yi ta kokarin daukar wasu hotunan.

Tun jiya ne kuma, wata tawagar Isra'ilan, wadda ta kunshi babban limamin addinin Yahudawa na sojin kasar, da wani likitan binciken gawawwaki, da dai sauran jami'an tsaro, ta iso a Kwalan. Jami'an sun zo ne dai don su tabbatar cewa, lalle gawawwakin sojojin Isra'ilan ne aka kawo musu. Bayan da suka tabbatad da hakan ne kuwa, aka bari fursunonin kasashen Larabawan suka sauko daga jirgin da ya dauko su daga birnin Tel Aviv. Ba da wani bata lokaci ba dai, sai aka kai su cikin jirgin saman rundunar sojin Bundeswehr ta Jamus, wanda kuma zai mai da su birnin Beirut na kasar Lebanon. A daya bangaren kuma, jirgin rundunar mayakan saman Isra'ilan zai koma Tel Aviv ne dauke da dan kasuwan Isra'ilan da aka sako, da kuma gawawwakin sojojin kasar guda 3.

A cikin larabawan da aka sakon, har da wasu muhimman shugabannin darikar shi'ite guda biyu- Sheikh Abed Karim Obeid da Mustafa Durani, wadanda Isra'ilan ta yi garkuwa da su tun shekaru da dama da suka wuce, don idan bukata ta kama kamar dai yanzu, ta yi musayarsu da `yan kasarta.

Babban jami'in kungiyar leken asirin Jamus, Ernst Urlau, wanda ya shiga tsakani ya kuma shirya wannan musayar, zai gamsu kwarai da sakamakon da aka cim ma yau. Amma duk da wannan nasarar, ba za a iya cewa, an tinkari kawo karshen tashe-tashen hankulla a Gabas ta Tsakiya ba ke nan. Harin baya-bayan nan da aka kai a birnin kudus dai na nuna yadda har ila yau, ake cikin wani hali na hauhawar tsamari a yankin. Muddin kuwa bangarorin biyu na ci gaba da yin garkuwa da mutanen da suka kame, to ba za a iya samun sassaucin al'amura ba.

Bugu da kari kuma, musayar fursunonin da aka yi yau dai, ba zai sami wani angizo kan shawarwarin zaman lafiyar da suka cije ba. Rawar da Jamus ta taka a wannan musayar kuma, kamata ya yi a dauke ta kamar wani taimako ne na kare hakkin dan Adam kawai, amma ba wani sabon babi na bai wa birnin Berlin wani muhimmanci a harkokin siyasar yankin Gabas Ta Tsakiyar ba. Babu shakka, Jamus na da kyawawan huldodi da duk bangarorin da rikicin Gabas Ta tsakiyan ya shafa. Kuma ta hakan ne ta cim ma nasarar shirya wannan musayar fursunonin, saboda amincewar da bangarorin suka yi da ita. Ban da dai sasantawar da ta yi tsakanin Hizbullah da Isradila, Jamus tana da kuma kyakyawar hulda da Iran. A yunkurin cim ma yarjejeniyar musayar fursunonin da ya yi, jami'in gwamnatin Jamus Ernst Uhrlau, ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa birnin Teheran.

A halin yanzu dai, Jumhuriyar Islama ta Iran da Isra'ila ba sa ga maciji da juna. Amma duk da haka, kasashen biyu na sha'awar ganin cewa, an sami wata tuntuba tsakaninsu, ta kan masu shiga tsakani. Ita Iran dai, tana neman sanin makomar wasu jami'an diflomassiyanta da suka bace a Lebanon. Isra'ila kuma, har ila yau ba ta da wani karin bayani game da wasu `yan kasarta guda hudu, wadanda su ma a kasar Lebanon din ne aka rasa alamunsu.

Ana nan dai ana kokarin cim ma wani daidaito kuma, don sake yin wata musayar fursunonin a karo na biyu, inda ake sa ran Isra'ilan za ta sako dimbin yawan larabawan da take tsare da su a gidajen yarinta.

Darasin da masu hura wuta a Gabas Ta Tsakiyan ya kamata su gane a nan dai shi ne; ko mene ne ma gurin da suka sanya a gaba, ba za su iya cim masa ta hanyar tashe-tashen hankulla ba.


 • Kwanan wata 29.01.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmD
 • Kwanan wata 29.01.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmD