Kotu ta saki shugaban IRA mai fafutuka a Murtaniya
May 18, 2016Magoya bayan shugaban kungiyar ta IRA Biram Ould Dah Ould Abeid da mataimakinsa Brahim Ould Bilal sun barke da murna bayan daka bada umarnin sakinsu daga inda ake tsare da su. Da ya ke tsokaci kan sakin na mutanen biyu, lauyansu Brahim ould Ee Betty ya ce:
"Kotun koli ta soke matakin tsare su bisa hujjar cewa kotunan biyu da suka dauki matakin tsare 'yan fafutkar su biyu a baya, sun yi aiki ne da wani kudirin doka da bai dace ba."
A jawabinsa na farko jim kadan bayan fitowarsa daga kurkuku, Biram ya bayyana farin cikinsa da wannan saki da aka yi masa kuma ya kara da cewa mawuyacin halin da suka tsinci kansu shi da abokin gwagwarmayar tasa a cikin zaman kason bai sanya zuciyoyinsu suka karaya ba game da aniyarsu ta ci gaba da wannan kokawa tasu.
Guda daga cikin 'yan kungiyar da ke cikin wanda ke son cigaba da fadi tashin da suke yi Balla Toure ya ce:
''Za mu ci gaba da kokawar yaki da bauta da ta kwace filayen noma da ake yi wa jama'a da duk wasu nau'o'i na bauta da na nuna banbancin launin fata dama na nuna wariya, domin mun yi imani cewa kokawar kwatar 'yanci ce kuma haka shi ne mafi alkhairi ga kasar Murtaniya"