1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye ta kashe yara biyu a Turkiya

January 5, 2006
https://p.dw.com/p/BvDk

Jamian kasar Turkiya sun tabbatar da cewa an samu wasu mutane dauke da kwayar cutar murar tsuntsaye a gabashin kasar.

Likitoci sunce yanzu haka yara biyu yan gida daya dan shekaru 14 da wata yar shekara 15 sun rasu, sakamakon wannan cutar.

Wadannan sune mutane na farko da suka kamu da cutar a wajen kudancin Asiya da Sin.

Kwayar cutar ta kashe akalla mutane 70 a gabashin Asiya tun shekarar 2003 ta kuma tilasta kashe miliyoyin tsuntsaye.

Kasar Turkiya da take yawan samun bakin tsuntsaye da ake ganin sune suke yada kwayar cutar,ta samu bullar cutar har sau biyu tsakanin talo talo da kaji da take kiwo cikin watanni 3 da suka shige.

A halin yanzu dai yawancin kasashen turai sun haramta shigo da kaji masu rai daga kasar Turkiya kodayake wasu kasashen sun sassauta wannan doka.