1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye na ci-gaba da bazuwa a kasar Turkiya

January 10, 2006
https://p.dw.com/p/BvCu

Kafofin yada labarun Turkiya sun rawaito cewar an sake gano kwayoyin cutar murar tsuntsaye a jikin wani dan kasar, abin da ya sanya yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar sun kai mutum 15. To sai dai har yanzu hukumomin kasar ba su tabbatar da wannan labarin ba. An dai gudanar da gwajin ne akan wasu majiyata 8 a lardin Sivas dake tsakiyar kasar. A cikin makon jiya nau´in H5N1 na cutar murar tsuntsaye yayi sanadiyar mutuwar kananan yara 3 a cikin kasar ta Turkiya. Jami´in MDD na musamman dake kula da masassarar tsuntsaye David Nabarro ya ce ga alamu dukkan wadanda cutar ta rutsa da su a Turkiya sun harbu da kwayoyin H5N1 din ne kai tsaye daga tsuntsaye dake dauke da cutar amma ba daga ´yan Adam ba. A kuma halin da ake ciki Jamus ta tsananta bincike akan iyakokin ta don hana shigowa da kaji cikin kasar ta barauniyar hanya.