Murar tsuntsaye na bazuwa a kasar Turkiya | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Murar tsuntsaye na bazuwa a kasar Turkiya

Kasar Turkiya ta ba da rahoton sake kamuwa da murar tsuntsaye karo na 4 ga dan adam a gabashin kasar. To sai dai kawo yanzu ba´a sani ba ko mutum na 4 da ya kamu da cutar na dauke da nau´in H5N1 na cutar matsanaciyar murar mai kisa, wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu yara biyu ´yan gida daya a wannan yanki a cikin makon jiya. Sakamakon binciken da aka gudanar akan wata yarinya da ita ma ta rasu bai tabbatar da nau´in kwayoyin na H5N1 ba. Wannan dai shi ne karon farko da ´yan Adam suka rasu sakamakon murar tsuntsayen a wajen nahiyar Asiya, inda akalla mutane 70 suka rasu sakamakon kamuwa da cutar tun bullar ta a shekara ta 2003.