Murar tsuntsaye a koriya ta kudu | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Murar tsuntsaye a koriya ta kudu

Yau ne jamian kula da harkokin kiwo na kasar Koriya ta kudu suka fara kashe kaji sama da dubu 200,bayan samun bullar murar tsuntsaye a wani gonan kaji a wannan kasa dake yankin Asia.Sakamakon hakane akesaran kashe dukkan kaji da dangoginsu kimanin dubu 236 a dukkan gonaki dake kewayen yankin da murar tsuntsayen ta bulla,domin dakatar da yduwar kwayar wannan cuta dake hallaka kaji.A makoin daya gabata nedai aka samu bullar murar tsuntsayen ,wanda ya haddasa mutuwan kaji dubu 13.Kasar koriya ta kudun dai ta kashe kaji da dangoginsu kimanin million 5.3,ayayin barkewar wannan cuta a shekarata 2003.