Murar tsuntsaye a Indonesia | Labarai | DW | 06.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Murar tsuntsaye a Indonesia

Rahotanni daga kasar Indonesia na nuni dacewa wata yarinya ta gamu da ajalinta sakamakon kamuwa da cutar murar tsuntsaye,wanda ya kawo ga adadin mutane 73 kena suka rasa rayukansu a wannan kasa kadai da bullar wannan cuta,inji jamian kasar da safiyar yau.Kakakin cibiyar nazarin cutar murar tsuntsaye dake kasar ta Indonesia ya tabbatar da cewa an samu kwayoyin cutar ajikin marigayiyar,wanda yayi sanadiyyar ajalinta a jiya alhamis.Yarinyar mai shekaru 15,tayi jinya na dan lokaci sakamakon kamuwa da cutar murar tsuntsaye.Bugu da kari wani dan kasar mai shekaru 29 da haihuwa ya gamu da ajalinsa a ranar laraba sakamakon kamuwa da cutar ta murar tsuntsaye.Ana dai kamuwa da murar tsuntsaye ne sakamakon alaka da tsuntsaye dake da wannan cutar,kai tsaye.