1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muradun yara a lokacin bukin Krisimeti

December 24, 2009

Wasu daga cikin shagulgulan bukin Krisimeti

https://p.dw.com/p/LD3q
Wurin aikewa da wasikun yara a KrisimetiHoto: DW

Gabannin bukukuwan Krisimeti, a sassa daban-daban na Duniya, yara kan rubuta wasiku inda suke bayyana muradan irin kyaututtuka da suke son samu tare da gabatar da wasu tambayoyi cikin wasikun da ke bukatar amsarsu.

Wani yanki dake gabashin birnin Koln dai na ɗaya daga cikin wuraren da amsoshin irin waɗannan wasiku ke fitowa. Domin a babbar majami'ar wannan gari ne ake da akwatin da wasikun ke zuwa, wanda kuma ke kasancewa ɗaya daga cikin manyan ofishoshin aikewa da wasiku shida dake faɗin tarayyar Jamus.

A wani ɓangaren wannan majali'ar ce dai ake da ofishin karɓa da aikewa da wasikun na chrisimeti. Amma menene dalilin kasancewar wannan ofishin a wannan haraba. Britta Töllner ita ce kakakin ofishin kula da wasiku.

Weihnachtspostamt in Engelskirchen 2009 Flash-Galerie
Wasikun KrisimetiHoto: DW

" Tun a shekara ta 1985 aka buɗe ofishin. Kuma hakan nada nasaba da cewar wannan wasika ce ta musamman da ake aikewa zuwa wuri guda. Bamu san yadda zamu yi dasu ba. Kuma da yake su anan majami'ar suna da kirki sosai, akwai isasshen lokacin da zasu tura zuwa sauran majami'un dake Britaniya. Kuma akwai wasu jami'an dake buɗe wasikun , su yi nazarin tambayoyin, da kuma bukatun yaran, kafin su aike musu"

Wasikun dai sukan taru a daidai wannan lokaci na bukukuwan chrisimeti, sa'annan sai ma'aikatan su tafi da su gida inda sukan buɗe su domin yin nazarin irin amsoshi da zasu aikewa yaran dasu.

A bara dai kimanin irin waɗannan wasiku dubu 145 aka aike zuwa wannan majami'a dake yankin gabashin birnin Koln. Kuma ana saran cewar a wannan shekarar wasikun zasu fi haka. Birgit Müller dake kasancewa ɗaya daga cikin jami'an dake kulawa da wasikun yaran na chrismeti, ta buɗe jakar wasikun domin nuna misalin abunda yaran ke rubutawa...

" wannan wasika ce daga wajen wata yarinya mai suna Pauline, ɗauke da hotonta data ɗauka da farin kare. Ta ce tana da babban muradi,wanda shine mallakar kyakkyawan kare. Alal misali daga cibiyar renon karnuka da ke kusa da birnin Hannover. Idan har aka samu sai a tuntuɓeni ta wannan lambar waya... kuma a nan ta rubuta lambobin da za a same ta...

Wannan kuwa wasika ce daga wani Felix wanda yake cewa, nasan cewar abunda nake muradi ya shige Euro 10, domin ina bukatar na'urar alam ce daga kamfanin Spytec. Amma zan yi matukar farin ciki idan da za a cika min burina na wallakar wannan na'ura. Domin har zuwa wannan makon ne ake sayar da na'urar akan farashin ragi"

Weihnachtspostamt in Engelskirchen 2009
Hotunan da ake aikewa da suHoto: DW

Haka dai waɗannan wasiku ke cigaba da zuwa daga yara daban-daban da bukatunsu a daidai wannan lokaci na Chrisimeti. Ayayinda wasu ke muradin samun kyautar muhimman abubuwa na taimaka musu, wasu na bukatar samun kayayyakin wasa ne. Kuma kowane yaro yana da 'yancin aikewa da wannan wasika da gabatar da tambayoyinsa akan abunda yake muradi a daidai lokaci kamar wannan na bukin Chrisimeti.Kuma a dukkan lokuta masu kulawa da wasikun yaran na iyakar kokarinsu na ganin cewar sun cikantawa yaran burin su.Wa Yaran muhimmancin Chrisimeti shine amsar tambayoyinsu da kuma samun waɗannan bukatu nasu.

Mawallafa: Birkenstock Günther/ Zainab Mohammed

Edita: Yahouza Sadissou Madobi