1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murabus din sakatare-janar na jam'iyyar CDU a Jamus

December 23, 2004

A sakamakon wata tabargaza ta karbar albashi ba a bisa ka'ida ba sakatare-janar na jam'iyyar CDU Laurenz Meyer ya sauka daga kan mukaminsa

https://p.dw.com/p/Bve2

Da farko dai shugabar jam’iyyar CDU Angela Merkel ta tsaya wa sakatare-janar Angela Merkel tana mai ba shi goyan baya domin ya ci gaba da rike mukaminsa. Amma a sakamakon matsin lamba mai tsananin da ta fuskanta daga saurna wakilan jam’iyyar sai ta ba da kai bori ya hau, shi kuma Meyer ya ba da sanarwar murabus dinsa bayan shekaru hudu da yayi yana rike da mukamin sakatare-janar na jam’yyar ta Christian Democratic Union. A lokacin da yake jawabi Laurenz Meyer cewa yayi:

Bayan nazari mai zurfi da nayi na lura cewar ci gaba da yi wa jam’iyyar aiki zai zama illa a gare ta. Bugu da kari kuma radadin dake tattare da iyali da kuma abokai na ya kai intaha, a sakamakon haka na tsayar da shawarar daukar wannan mataki a cikin gadin gaba.

Wakilan reshen jam’iyyar ta CDU a nan jihar Northrhine-Westfaliya da na jihar Schleswig-Holstein dake kuryar arewacin Jamus su ne suka fi yin matsin lamba wajen ganin lalle sai Laurenz Meyer ya sauka daga mukamin nasa na sakatare-janar ta la’akari da zabubbukan da za a gudanar na majalisun jihohin guda biyu a farkon shekara mai zuwa. Kuma a ganin jami’an siyasar jihohin tabargazar ta Laurenz Meyer zata zame musu kayar kifi a wuya a matakansu na yakin neman zabe. Ita kanta shugabar jam’iyyar ta CDU Angela Merkel daga bisani ta hakikance da gaskiyar cewa dagewa akan ba wa Meyer goyan baya zai kai jam’iyyar ya baro, a sakamakon haka tayi marhabin da shawararsa ta murabus duk da kyakkyawan hadin kan da ya wanzu tsakaninsu a cikin shekaru hudun da suka wuce. Ta dai gabatar da Volker Kauder daga jihar Baden-Württemberg domin ya maye gurbinsa. A lokacin da yake jawabin amincewa da nadin da aka yi masa Volker Kauder cewa yayi:

Zan rike wannan mukamin da hannu biyu-biyu, in kuma yi aiki tukuru dangane da manufar da muka sa gaba. Manufar kuwa ita ce ta nada wata nagartacciyar gwamnati a nan kasar a shekara ta 2006.

Duk da wannan tabargaza dukkan wakilan jam’iyyar CDU sun yaba da aiki tukuru da Laurenz Meyer yayi wa jam’iyyar a cikin shekaru hudun da suka wuce sannan suka yi madalla da shawararsa ta murabus saboda hakan zata ba su cikakkiyar dama ta dukufa akan yake-yakensu na neman zabe a zabubbukan jihohin na Northrhine-Westfaliya da Schleswig Holstein a shekara mai zuwa.