Murabus ɗin Firimiyan Japan | Labarai | DW | 02.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Murabus ɗin Firimiyan Japan

A wani abinda ke nuna kasawa bisa cika alƙawarin da ya yi wa 'yan ƙasar, Firimiyan ƙasar Japan yasanar da cewa zayyi murabus

default

Yukio Hatoyama

Firayim ministan ƙasar Japan Yukio Hatoyama ya sanar da cewa zai ajiye aikinsa, watanni tara bayan kama aiki. Firimiyan dai yana fiskantar matsin labba daga jam'iyarsa, da sai ya sauka gabanin zaɓen 'yan majalisar dattawan ƙasar da za'a gudanar a watan gobe. Gwamnatinsa ta samu koma baya daga shawa'awar da 'yan ƙasar ke mata, tun bayan kama mulki a bara. Inda 'yan ƙasar ke cewa dama ya yi musu alƙawarin rufe sansanonin sojin Amirka dake tsibirin Okinawa, amma yakasa yin hakan, abinda kuma ya jawo masa mummunan baƙin jini.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu