1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murabus ɗin ministan tattalin arzikin Jamus

Mohammad AwalFebruary 9, 2009

Bayan murabus ɗin da ministan kula da tattalin arzikin ƙasar Jamus Michael Glos yayi, shugabannin siyasar ƙasar na ci gaba da maida martani bisa hakan.

https://p.dw.com/p/Gq3a
Michael Glos tsohon ministan tattalin arzikin JamusHoto: AP

Sanarwar da ministan ya bayar ta zo ne a lokacin da tattalin arzikin kasashen duniya yake ƙara shiga uku. Michael Glos ya bada wannan sanarwar ne bayan da ya gana da jam'iyarsa ta Christain Social Union a birnin Munich dake zaman helkotar jam'iyar tasa. Ga abinda ya fara cewa.

"Ina mikawa shugabar gwamnati takarda ta murabus da kuma sunan mai maye gurbina, wanda shugaban jam'iyarmu zai fadi sunansa dan ba da sanawar kawonane idan aka zaɓa don maye gurbin nawa."

Kafafen yaɗa labaran ƙasar ta Jamus sun rawaito cewa mai yuwa ne a maye gurbin ministan da babban sakatare na jam'iyarsa ta Christain Social Union Karl-Theodor zu Guttenberg. Kana kuwa nan take shima an fito da sunan wanda zai maye gurbinsa a matsayin sabon babban sakataren Jam'iyar ta CSU.

Karl-Theodor zu Guttenberg wird Nachfolger von Bundeswirtschaftsminister Michael Glos
Karl-Theodor zu GuttenbergHoto: AP

A nasa martanin ministan harkokin wajen Jamus kuma ɗan takaran neman kujerar shugaban gwamnatin Jamus ƙarƙashin inuwar jam´iyar SPD a zaɓe mai zuwa nan gaba a wannan shekara, Frank-Walter Steinmeier yace wannan murabus ɗin ministan bai zo masa da mamaki ba.

"A wannan yanayin na taɓarɓarewa tattalin arziki, ba dai dai bane ma muyi ta tattauna batun minstan tattalin arziki na gaba. Ai wannan batune da ya shafi yan jami'iyar CSU, su ya kamata su bayyana shi."

Yanzu haka dai ta bayyana cewa Karl-Theodor zu Guttenberg shine aka miƙa sunansa don maye gurbin mistan tattalin arzikin kasar ta Jamus. Guttenberg matashi ɗan shekaru 37 da haifuwa yana ɗaya daga sabbin jini a siyasar ƙasar ta Jamus. an zabe a majalisar dokokin Jamus yana dan shekaru 30. A watan Nowamban da ta gabata ne aka zaɓe mukamin sakatere janar na jam'iyar CSU mai gawanci da jami'iyar shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel.

Wannan murabus ɗin ministan tattalin arzikin Jamus ya zo ne a lokacin da ƙasar wadda tafi kowacce ƙasa ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Turai, take cikin wani halin taɓarɓarewar tattalin arzikin da bata gani ba tun yaƙin duniya na biyu. Bugu da ƙari yanzu sauran watanni bakwai a gudanar da zaɓen majalsar dokokin tarrayar ƙasar ta Jamus wato Bundestag.