1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mura aladdai ta fara zama annoba.

April 28, 2009

Annobar mura aladdai ta fara tada hankula a duniya.Matakan riga kafi da ƙasashen Afirka ke ɗauka

https://p.dw.com/p/Hg4o
Murra alladaiHoto: AP

Hankullan ƙasashen duniya na cigaba da kaɗuwa a game yaduwar sabuwar annobar nan ta mura aladdai da ta kunno kai a ƙasar Mexiko.

Ƙasashe dabam dabam na duniya sun fara ɗaukar matakan riga kafi.

Wannan cuta ta murra alladai da ta ɓarke a ƙasar Mexiko tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 150, kuma ta na cigaba da bazuwa babu ƙaƙƙabtawa.

Saboda haka ne ƙasashe dabam dabam na duniya suka fara ɗaukar matakai da zumar killace ta.

Wannan matakai sun haɗa da ƙarfafa binciken kiwan lafiya a filayen saukar jiragen sama, mussaman ga fasenjojin da suka hito daga yankin Latine Amurika.

A ɗaya hannun wasu ƙasashe sun dakatar da shigo da naman alladai da dangoginsa, duk kuwa da cewar ƙurrarun likitoci sun tabbatar da ba a kamuwa da cutar ta hanyar cin naman aladai.

A nahiyar Afrika, duk da cewar cutar ba ta bula ba,tunni ƙasashe sun fara shiga shirin ta kwana.

Ƙasashen da suka riga suka ɗauki matakai, ya zuwa wannan lokaci sun haɗa da Maroko,Masar, Gana Afrika ta Kudu Zambiya da Mozambik.

Hukumomin Marroko alal misali sun yanke shawara tsaurara bincike lafiya a tashoshin jiragen ruwa filayen saukar jiragen sama da iyakokin ƙasar.

A nasu ɓangaren hukumomin filin saukar jiragen sama birnin Alƙahira, sun daɗa sa ido tare da yin binciken ƙwaƙƙwap ga dukkan fasenjojin da suka hito daga Mexiko.

Ƙasar Ghana a nata gefe, ta haramta shigo da naman alladai kwata kwata, sannan hukumomin sun girka komiti na mussamman da aka ɗorawa yaunin bin diddiƙin halin da ake ciki, a game da cutar murra alladai.

Wannan matakai riga kafi, sun yi kama da wanda hukumomin Afirka ta Kudu da Zambiya suka ɗauka.

Saidai daga dukkan ƙasashen Afirka, Mozambik ta fi ɗaukar matakai masu tsauri, domin fadar gwamnatin Maputu, ta kafa abunda ta raɗawa suna dokar ta ɓace a akan wannan cuta.

Daraktan hukumar kiwan lafiya ta ƙasa Leonardo Chavane ya tabbatar da cewar sun lunka bincike a kan duk mutanen dake fama da rashin lafiya, sannan sunyi tanadi na mussamman, a tashoshin jiragen ruwa.

Ya zuwa yanzu dai daga jimlar mutane 1.600 da aka haƙiƙance cewar sun kamu cutar murra alladi a Mexiko, fiye 150 da suka rasa rayuka.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed T.Lawal