1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika A Jaridun Jamus

June 21, 2009

Sojojin Mali na ɗaukar matakan murƙushe wata ƙungiyar 'yan ta-kife dake kiran kanta wai ƙungiyar Al-Ƙa'ida mai ta da zaune tsaye da karkashe bayin Allah ba gaira ba dalili.

https://p.dw.com/p/IVkG
Yankin Hamada na garin Timbuktu a MaliHoto: DW / Debrabandère

A wannan makon dai ko da yake kafofin yaɗa labaran Jamus baki ɗaya sun fi mayar da hankalinsu ne akan halin da ake ciki a ƙasar Iran bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar makon da ya wuce, amma duk da haka sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran Afurka. Misali jaridar Die Tageszeitung, wadda ta leƙa ƙasar Mali domin bitar matakan da sojojin ƙasar suke ɗauka a fafutukar murƙushe wata ƙungiyar ta 'yan ta-kife dake kiran kanta wai ƙungiyar Al-Ƙa'ida mai ta da zaune tsaye da karkashe bayin Allah ba gaira ba dalili. Jaridar ta ce:

"A karon farko sojojin Mali sun kai hari kan wani sansani na ƙungiyar 'yan ta'adda dake kiran kanta wai ƙungiyar al-ƙa'ida ta musulmin maghreb dake shirya ayyukanta a wani yanki na hamada dake arewacin ƙasar ta Mali. A makon da ya gabata dakarun ƙungiyar suka kutsa garin Timbuktu suka halaka wani babban jami'in soja a gidansa. Tun daga sannan gwamnatin Mali ta lashi takobin saka ƙafar wando ɗaya da ƙungiyar, wadda a yanzu haka ake shawartawa tsakanin ƙasashen Mali, Mauritaniya, Aljeriya da Nijer don neman hanyar murƙushe ta."

Holzverkauf in der Hauptstadt Bamako, Mali
Ƙunshin itace a Bamako, MaliHoto: DW / Debrabandère

A wani sabon ci gaba kuma ƙasashen Turai na shawarar kashe abin da ya kai Euro miliyan dubu ɗari huɗu don kafa wata tashar makamashi daga hasken rana a yankunan hamadan Afurka. Jaridar Der Tagesspiegel ta ba da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Fatan ƙasashen Turai shi ne samun kashi 15 cikin ɗari na makamashin da suke aiwatarwa daga wannan tasha, wadda ake fatan zata fara aiki daga shekara ta 2020."

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung sharhi tayi akan wannan manufa tana mai cewar:

"Da farko dai zaka ji maganar kamar tatsuniya, amma fa a haƙiƙa akwai cikakkiyar kafa ta wanzar da wannan shiri, saboda kafa tashar ba abu ne mai wuya ba kuma haske rana wata albarka ce daga Indallahi. Bugu da ƙari kuma aiwatar da wannan shiri zai taimaka wa matakan da ake ɗauka na kawo ƙarshen matsalar ɗimamar yanayi da kuma kare makomar kewayen ɗan-Adam. Amma a inda take ƙasa tana dabo shi ne barazanar da butututan da wutar lantarkin zata riƙa bi cikinsu zuwa nahiyar Turai. Domin kuwa ƙasashen da lamarin ya shafa zasu iya yin amfani da wannan dama don matsin lamba kan kasashen Turai akan wasu buƙatunsu."

Zusätzliche Kongo Truppen möglich
Sojin Kongo a kusa da sansanin KibatiHoto: picture-alliance/ dpa

A can ƙasar Kongo har yau ana fama da mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi, inda kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta nunar da zarar gwamnati ta cimma daidaituwa da wata ƙungiya ta 'yan tawaye, sai wata sabuwar ƙungiyar kuma ta ta da ƙayar baya. Jaridar ta ce gabacin Kongo na daɗa nutsewa cikin kogin tashe-tashen hankula a yayinda a ɗaya ɓangaren kuma ake daɗa samu yawan tagayyararru da kan yi hijira daga yankunansu.

Mawallafi: Ahmadu Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal