Munanan hare hare a kasar Iraki | Siyasa | DW | 14.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Munanan hare hare a kasar Iraki

A yau an wayi gari da munanan hare hare da sukayi sanadin mutuwar mutane kusan 100 a Iraki

default

Wani bam cikin mota ya fashe a wani lardin yan shia a birnin Bagadaza,a safiyar yau laraba,inda yayi sanadiyar mutuwar mutane a akalla 80 wasu 109 kuma suka samu rauni.

A wani rahoton na daban kuma wasu yan bindiga sun kashe mutane 17 a yau din a garin Taji arewacin Bagadaza.

Yan sanda sun ce,yan bindigan sun janyo mutanen daga gidajensu kana suka harbe su a kofar gidajen nasu.

An kai wasu hare hare guda hudu kann sojojin Amurka,sojinIraki hudu sun rasa rayukansu ciki.

Kashe kashen irin wannan yana kara tada hankulan jamaa game da barkewar yakin basasa a kasar ta Iraqi,yayinda sojin sa kai kw kokarin ganin sun tunbuke gwamnatin kasar da Amurka ke marawa baya.

 • Kwanan wata 14.09.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZe
 • Kwanan wata 14.09.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZe