1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mummunar gobara a Girka

August 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuD1

Mummunar gobaran nan da ta ɓarke a ƙasar Girka, na ciga ba da hadasa ta´adi a sassa daban-daban.

Ya zuwa yanzu, mutane a ƙalla 61 a ka tabbatar da sun ƙone ƙurmus, da kuma assara dukiya mai ɗimbin yawa.

Wannan gobara, da ta yi kama da irin wadda bahaushe ke dangatawa da goba da daga kogi maganin ki Allah, itace mafi muni a dunia baki ɗaya, tun fiye da shekaru 150 da su ka wuce.

A halin yanzu gwamnatin ƙasar Girka ta kiɓice, ta kuma yi kira da babbar murya ga ƙasashen dunia su bata lallafi.

Jamus, France , Italia da sauran ƙasashen EU, sun aika jiragen kashe wuta,da takuna.

A sakamakon wannan taron dangi, rahottani daga ƙasar sun ce a halin da ake ciki, an fara cimma nasara kashe wannan gobara.

Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da mussababin ɓarkewar gobara ba, saidai su na hasashen cewar, ba ta rasa nasaba da ayyukan ta´adanci.