1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mummunar girgizar kasa a arewacin Chile

A ɗazu ɗazun nan, arewacin ƙasar Chile ya fuskanci wata mummunar girgizar ƙasa.Rahotanni sun sanar da cewa girgizar ƙasar, ta kai tsawon mita 7 da ɗigo 7 a ma´aunin rishta.Tuni dai wannan al´amari ya haifar da katsewar wutar lantarki, a gurare da daman gaske a yankin. To sai dai ya zuwa yanzu, babu bayanin salwantar rai ko kuma cikakken bayanin irin ɓarnar data haifar.