Mujallar Mikses don inganta zamantakewa | Zamantakewa | DW | 02.10.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mujallar Mikses don inganta zamantakewa

Mujallar dai za ta canza taswirar yaɗa labaru a cikin Jamus kuma tana zama muryar matasan ƙasar.

default

Mari Böhmer wakiliyar wgamnati mai kula da batutuwan sajewar baƙi

A cikin shirin na wannan makon za mu duba wata sabuwar muhalla ce da ake kira Mikses wadda aka fara bugawa da nufin bawa fannin yaɗa labaru da aikin jarida a Jamus sabon salo. Hakazalika mujallar ta Mikses na matsayin wata muryar matasa a cikin wata gamaiya da ta ƙunshi al´adu daban daban.


Kamar yadda na nunar a shimfiɗar shirin, mujallar ta Mikses na matsayin wata kafar ba da labarai da rahotanni na siyasa, zamnatakewa, nishaɗantarwa da kuma ainihin halin da ake ciki musamman na cuɗanya tsakanin mabiya al´adu daban daban a nan Jamus. Editocin wannan mujalla, matasa maza da mata suna mayar da hankali akan muhawwarorin da ake yi game da addinin Musulunci da tsarin zamantakewa da zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka. Wata Bajamushiya ´yar asalin ƙasar Turkiya Ikbal Kilic ta ƙirƙiro wannan mujalla ta yi bayani dangane da burin da suke son cimma.


1. Ikbal kilic:

“Tun wasu shekaru da dama da suka wuce muke da wannan ra´ayi, wato samar da wata kafar yaɗa labaru da za ta zama akasin abubuwan da aka saba ji daga mafi yawancin kafofin yaɗa labaru. Sanin kowa ne dai cewa ɗaukacin kafofin yaɗa labarun da sauran ´yan jarida sun fi ba da muhimmanci ga matsalolin da ake fuskanta musamman a ɓangaren zamantakewa tsakanin al´adu daban daban. Amma mujallar Mikses za ta duba dukkan ɓangarorin ne gaba ɗaya tare da rawaito abubuwan da ke wakana a rayuwa ta yau da kullum. Ko da yake mu ɗin ma za mu taɓo matsalolin da ke akwai amma ta hanya mafi dacewa, wadda ba safai ake samu a nan Jamus ba.”


Kimanin shekara guda da ta gabata Ikbal Kilic ´yar shekaru 27 da haihuwa ta ƙirƙiro mujallar ta Mikses game da cuɗanya tsakanin mabiya al´adu daban daban a Jamus. Ana buga mujalla mai shafuka 86 a cikin harshen Jamusanci. Baya ga rahotanni masu ƙayatarwa dake ƙarin haske akan batutuwan da suka shafi al´adu ana ƙawata mujallar da hotuna masu ban sha´awa waɗanda ke ɗaukar hankalin mai karatu. A ganin farko ana yiwa mujallar kallon irin mujallun nan na masu sha´awar tsarin rayuwa na zamani, amma idan aka dubata da idanun basira za a ga cewa ta ƙunshi rahotanni masu yawa game da zaman tare tsakanin Jamusawa da baƙi.


Mujallar ta na mayar da hankali kan wani sabon salo na tsarin zamantakewa. Elvin Türk wadda ita ma ´yar asalin ƙasar Turkiya ce dake aikin tsara mujallar ta yi bayani kan abin da suke nufi da sabon tsarin zamantakewa da cewa suna magana ne game da matasan musulmi.


2. Türk:

“Mun yi amfani da wannan kalma ta sabon tsarin zamantakewa domin a cikin wannan lokacin ba bu wani misali mafi dacewa da zai yi ƙarin bayani kan zaman cuɗe-ni cuɗe-ka domin mu riga mun saje da ´yan ƙasa. Da yawa daga cikinmu wato kimanin kashi 99 cikin 100 a nan aka haife mu, a nan muka tashi a nan muka yi wayo. Shi ya sa a gare mu maganar sajewa ma ba ta taso ba, domin mu ´yan ƙasa ne.”


A rahotanninta mujallar ta fi mayar da hankali a fannonin siyasa, zamantakewar al´umma da rayuwar ɗalibai a jami´o´i. Hakazalika tana kuma ba da rahotannin masu gamsarwa game da addinin musulunci da kuma Jamusawa Musulmi. A cikin wani salsalar shirye shirye mai taken “da me duniya ta yi imani” mujallar na gabatar da tambayoyi masu muhimmanci ga addini ga masana kan batutuwan addini na manyan addinai biyar a duniya. A kashin farko na shirin an yi bayani ne dalla-dalla game da addinin musulunci, wato kamar shika-shikan addinin na musulunci.


Da farko an fara buga mujallar ne da kofi dubu 10 dake fita sau huɗu a shekara wato bayan ko waɗanne watanni uku-uku. Ana samun kuɗi yin wannan aiki ne ta hanyar tallace-tallace da sayar da filin talla a cikin mujallar. Nan gaba kaɗan za a fara bugata ta yanar gizo wato intanat domin ta kai ga matasa da yawa cikin sauƙi. Mujallar ta Mikses na zaman wata muryar matasa a nan Jamus, waɗanda tuni sun rigaya sun saba da zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka tsakanin mabiya al´adu daban daban.


Editoci 19 ke aiki a kamfanin buga mujallar cikin su har da Jamusawa waɗanda ba su da dangantaka da ƙasashe wajen sai kuma Jamusawa masu asali da Turkiya wato kamar Ikbal Kilic da kuma Ervin Türk. Ana kuma buga rahotanni masu yawa a cikin mujallar dake ɗaukar hankalin matasa musamman ´ya´yan Turkawa da suka zama Jamusawa. Ko shin mujallar ta Turkawa ce ga ´yan Turkiya dake Jamus. Ikbal Kilic ta yi bayani tana mai cewa.


3. Ikbal Kilic:

“Ko shakka babu wannan batun shi ya fi ɗaukar hankali a mujallarmu ta farko. To amma jigon rahotanninmu ya yi nuni da cewa ba mu taƙaita aikinmu akan gamaiyar Turkawa kaɗai ko akan Jamusawa masu asali da Turkiya ko akan Jamusawa kaɗai ba, a´a mun ba da muhimmanci ga dukkan ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki a batun da ya shafi cuɗanya tsakanin al´adu daban daban.”


Jigon rahotannin da mujallar ta fara bugawa na matsayin wani shiri ne, inda mujallar ta Mikses ta gabatar da wasu mutane masu al´adu daban daban waɗanda a yanzu suke ƙara ɗaukaka martabar Jamus. Daga cikinsu akwai mawallafan littattafai kamar Feridun Zaimoglu da masu gabatar da shirye shirye na telebijin kamar Aiman Abdallah da Charlotte Roche. Ga dukkan waɗannan mutanen batun asalinsu da baƙi ´yan ci-rani ba ya taka wata rawa kuma.


Waɗannan mutanen dai sune matasa sababbin jini a Jamus, kuma sune ke zama tamkar wakilan baƙi a kafofin yaɗa labaru. Ikbal Kilic ta yi ƙorafin cewa kafofin yaɗa labarun Jamus ba sa nuna yadda ake samun al´adu daban daban a cikin ƙasar. Hakan kuwa ya shafi muhawwarar da ake yi game da zaman-tare da kuma aadininin Musulunci.


4. Ikbal Kilic:

“Irin wannan matsala ake fuskanta a babban taro kan addinin musulunci a nan Jamus. Kimanin kashi 15 cikin 100 na waɗanda ke halartar taron ke wakiltar dukkan ƙungiyoyin musulmi kai tsaye. Ko da yake na san abu ne mai wuya gamaiyar musulmin gaba ki ɗaya ta samu cikakken wakilci a gun taron amma bai kamata a riƙa aron bakin wasu ana ci musu albasa ba. Dole su ma a ji ra´ayinsu.”


Masu buga mujallar sun ce ba za su kawad da idonsu daga zahirin abubuwan da ke faruwa ba a fannin zaman baƙi da nuna musu wariya da ƙoƙarin shigar da su cikin al´umma. Masu karanta mujallar sun banbanta. Ɗaukacinsu sun gamsu da batutuwan da mujallar ke mayar da hanakali kansu kamar wannan matar mai karanta mujallar:


“Mujallar Mikses ta nunar da cewa yanzu an shiga wani sabon dandalin tattaunawa game da zaman cuɗe-ni in-cuɗe-ka. Ta kuma nunar da cewa tuni an shiga wannan tattaunawa kuma har yanzu ana ciki ba tare da wata muhawwara game da addinin musulunci ba. Mujallar ta ƙunshi abubuwa da dama kuma ta na zaman kyakkyawan misali na tsarin zamantakewar al´ummomi daban daban a wannan ƙasa.”