Muhawarar majalisar dokokin Jamus kan waadin dakarunsu a Afghanistan | Labarai | DW | 20.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Muhawarar majalisar dokokin Jamus kan waadin dakarunsu a Afghanistan

Majalisar dokoki ta Jamus ta Bundestag ta fara muhawa akan batun kara waadin aiyukan dakarun Jamus a kasar Afghanistan.Ministan harkokin waje Frank Walter Steinmeier yace saboda matsannancin hali da ake ciki a kasar ta Afghanistan ya kamata mahukuntan Jamus su kara waadin aiyukan dakarun nasu.A yanzu haka sojojin na Jamus suna karkashin dakarun NATO ne haka kuma Jamus ta tura jiragen leken asiri guda shida zuwa kasar:Sai dai kuma jama a nan Jamus suna fara baiyana shakkunsu game da yiwuwar samun nasarar aiyukan dakarun na NATO,ganin irin tashe tashen hankula da rashin doka da oda dake ci gaba a kasar ta Afghanistan.A jiya ne dai MDD ta kara waadin aiyukan rundunar ta ISAF dake aikin wanzar da zaman lafiya a Afghansitan.