1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan zaman baki masu al'adu dabam a Jamus

October 11, 2010

Martani kan jawabin Pirimiyan Bavaria game da yan ci rani daga Turkiya da kasashen Larabawa

https://p.dw.com/p/Pba0
Pirimiyan jihar Bavaria, Horst SeehoferHoto: AP

Pirimiyan na jihar Bavaria, Horst Seehofer, lokacin da yake hira da mujallar Focus a karshen mako yace a fili yake, cewa yan ci rani masu wasu al'adun dabam dake shigowa nan Jamus, misali daga Turkiya ko daga kasashen Larabawa sukan sha wahala a game da kokarin su na sajewa da tsarin rayuwa a wannan kasa. Seehofer dai dan jam'iyar Christian Social Union ne, wato CSU a takaice, wadda ake iya cewa kanwa ce a jihar Bavaria ta jam'iyar Christian Democrats ta shugaban gwamnati, Angela Merkel. Pirimiyan na jihar Bavaria yace saboda haka ne ya kai ga ra'ayin cewar ba'a bukatar karin yan ci rani masu wasu ala'adun dabam da zasu yi ta kwarara zuwa Jamus. Kamar kuwa yadda akai zato, wannan ra'ayi ya yi ra samun adawa daga bangarori dabam dabam, alal misali daga magajin garin birnin Berlin, Klaus Wowereit, dan jam'iyar Social Democrats, wato SPD.

"Yace irin wannan jawabi babu shakka zance ne kawai na rashin tunani. Irin wadannan jawabai ne bama bukatar jin su a muhawarar dake gudana yanzu kan zaman baki da sajewar su a nan Jamus. Irin wannan jawabi daidai yake da kaskantarwa da cin mutuncin mutane dake zuwa mana daga wasu kasashe, wadanda kuma muke son zaman su a tare damu, wadanda suke tafiyar da rayuwar su da aiyukan su tare da cikakiyar nasara a kasar ta Jamus. Irin wannan jawabi kuskure ne.Yan siyasa suna da alhakin da ya rataya a wuyan su, ya kuwa kamata su lura da wannan nauyi dake kansu".

Shima shugaban jam'iyar Greens Cem Özdemir, ya kwatanta jawaban Seehofer a matsayin abin da ba za'a ce ya fito daga bakin mai hankali ba.

"A Jamus, ba zamu kai matsayin da zamu rika tankade da rairaya ga mutane bisa dacewa daga kasashen da suka fito ba. Mukan dauki mutane ne a matsayin masu son zama yan kasa da masu son su zauna tare damu kawai. Duk wani abin da ya wuce haka ba abin da ya shafi mu bane".

Taraiyar kungiyoyin Turkawa mazauna Jamus ta yi mumunan suka ga jawaban na Seehofer. Kenan Kolat, shine shugaban wannan taraiya.

"Yace da nayi zaton Seehofer dan siyasa ne mai mutunci da ya san abin da yake yi. Irin wadannan jawabai sukan zama kaskantarwa da cin mutunci da kuma bata sunan Jamus a idanun duniya. Ina sa ran shugaban gwamnati, Angela Merkel zata fito fili ta nuna rashin goyon bayan ta ga wadannan jawabai".

Goyon bayan da Seehofer kadai ya samu ya fito ne daga jam'iyar s ta CSU, wanda shugaban yan jam'iyar a majalisar dokokin taraiya, Hans Joachim Friedrich, a lokacin wata hira, yace abubuwan da Seehofer ya fadi daidai ne. Duk da haka, shi kansa Seehofer ya zuwa ranar Litinin ya fara shakkar gaskiyar abin da ya fada. Yace bai taba bude bakin sa ya nemi a dakatar da shigowar Turkawa da Larabawa nan Jamus ba. Abin da yace ya shafi kwararowar kwararrun ma'aikata ne daga ketare dake mamaye wuraren aikin yi a kasar. Saboda haka ne ma shugaban gwamnati, Angela Merkel take ganin ba sai ta dauki wani karin mataki na janye kanta daga Pirimiyan na jihar Bavaria ba.

Jam'iyar FDP dake hadin gwiwa da Angela Merkel a taraiya ta kwatanta jawabin na Seehofer a matsayin abin da ko kadan bai dace a daidai wannan lokaci ba. Kakakin jam'iyar, Christian Lindner yace ganin yadda jam'iyar ta CSU take rasa farin jinin ta, irin wadannan jawabai basu zama abin mamaki daga shugaban ta ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Abdullahi Tanko Bala