1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MUHAWARA KAN TURA DAKARUN JAMUS ZUWA IRAQI

YAHAYA AHMEDApril 16, 2004

Wata muhawarar da ta barke a bainar jama’ar Jamus, ita ce kan batun tayin da Usama bin Laden ya yi wa kasashen Turai, na kebe su daga ababan barar harin kunan bakin wake, idan suka janye dakarunsu daga kasashen musulmi. A halin yanzu dai, duk kasashen Turan sun yi watsi da wannan tayin. Amma a nan Jamus, jama’a na ta kara sanya alamar tambaya ga kiran da jam’iyyun adawa ke yi wa gwamnati, na ta tura dakaru zuwa Iraqi, idan bukatar hakan ta taso karkashin jagorancin kungiyar NATO da kuma Majalisar dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/Bvkc
Dakarun Bundeswehr, a kan hanyarsu zuwa Afghanistan
Dakarun Bundeswehr, a kan hanyarsu zuwa AfghanistanHoto: AP

A halin yanzu dai, babu sojojin Jamus a Iraqi. Amma dimbin yawan dakarun rundunar Bundeswehr na girke a Afghanistan da lardin Kosovo. Wasu masharhanta na ganin cewa, Jamus na da gaskiya a matsayin da ta dauka na yin adawa ga afka wa Iraqi da yaki, idan aka yi la’akari da tashe-tashen hankulla da halin rudamin da ake ta samu a wannan kasar a kwanakin bayan nan. Har ila yau dai, Jamus na kan bakanta, na kin tura dakaru zuwa Iraqin, ko da ma a karkashin laimar Majalisar dinkin Duniya ne.

Amma irin ababan da suka wakana a Iraqin a kwanakin bayan nan, sun sa wasu kasashen Turai sake tunaninsu game da tura dakaru zuwa kasar. Jamus ma ta ji sakamakon wannan rikicin a jika, yayin da `yan yakin sunkurun Iraqi suka kashe wasu jami’an tsaronta, na rukunin nan na GSG-9 guda biyu, a wani kwanton baunar da suka yi musu, a kan hanyarsu daga Amman zuwa Bagadaza. Tayin tsagaita wuta da shugaban kungiyar Al-Qa’ida, Usama bin Laden ya yi wa kasashen Turai bisa wasu sharudda kuma, na nuna cewa Jamus ma za ta iya zamowa abin barar ta’addanci.

Bin Laden dai ya yi kira ga kasashen Turan ne da su janye dakarunsu daga Iraqi da kuma Afghanistan. Idan sun yi hakan, to kungiyarsa za ta dakatad da kai musu hare-haren kunan bakin wake.

A ganin masu sukar lamiri a nan Turai kuwa, wannan tayin wato wani yunkuri ne da kungiyar Al-Qa’idan ke yi na rarraba kawunan kasashen Turan da Amirka. Kamar yadda aka zata dai, duk kasashen nahiyar, a cikinsu kuwa har da Jamus, sun yi watsi da tayin.

Ba abin mamaki ba ne kuma, ganin yadda wannan batun ya janyo barkewar wata muhawara a bainar jama’a a nan Jamus. Abin da ake tattaunawa yanzu dai shi ne, ko Jamus za ta tura dakarunta zuwa Iraqin, idan bukatar yin hakan ta kama ? Kuma, bisa wane tsari ne za a tura dakarun ? Jam’iyyun adawa na CDU/CSU a Majalisar dokoki ta Bundestag dai, sun nuna shirin amincewarsu da girke rukunan sojin Jamus Iraqin, duk da halin rudamin da ake ciki a kasar a halin yanzu. Shugaban reshen jam’iyyun a Majalisar, Wolfgang Schäuble ne ya bayyana wannan ra’ayin. Amma ko su ma `yan adawan, za su amince da tura dakarun ne kawai, idan yin hakan zai kasance karkashin laimar Majalisar dinkin Duniya da kuma kungiyar NATO.

Manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa, kafin ran 30 ga watan Yuni, wannan batun zai sake kunno kai a teburin shawarwarin `yan siyasa. A wannan lokacin ne dai Amirka ta ce za ta mika ragamar mulkin Iraqin ga gwamnatin wucin gadi ta `yan kasar. Idan ko hakan ya samu, to babu shakka, rundunar kungiyar NATO ce, za ta maye gurbin mafi yawan dakarun Amirka a kasar. A nan kuwa, Jamus ba za ta iya kauce wa nauyin da ya rataya a wuyarta, a matsayinta na `yar wannan kungiyar ba. Kasashen Turan gaba daya ma, za su sami kansu ne cikin wani hali na gaba kura, baya sàyáakíi.

A bangare daya, ba za su iya kai Amirkan su baro a kan wannan batun ba. Amma a daya bangaren kuma, Turawan ba sa son su kasance a idanun duniya, tamkar `yan amshin shatan Amirkan.

Tambayar da jama’a ke ta yi yanzu a nan Jamus dai shi ne, wai shin tilas ne a tura dakarun rundunar Bundeswehr a Iraqi kuwa, yayin da ga wasu daruruwan dakarun kuma har ila yau a Afghainstan da Kosovo ? Gwamnatin tarayya dai ta bayyana cewa, ta ba da matukar gudummuwar da za ta iya bayarwa, da tura dakarunta zuwa Afghanistan da yankin Balkan, karkashin shirin nan na yakan ta’addanci a duniya. Yannzu kam, kamata ya yi, a bukaci wasu kasashen kuma, don su ma su dau nauyin da ya rataya a wuyarsu, a wannan manufar da aka sanya a gaba.

Idan aka yi la’akari da halin da ake ciki yanzu a Afghanistan, da kuma irin barazanar da madugan yakin kasar ke yi wa yunkurin samad da zaman lafiya da gamayyar kasa da kasa ke yi, to lalle za a ga cewa, sai an shafe shekaru da dama kafin kurar rikici ta lafa a wannan kasa. A duk tsawon wannan lokacin kuwa, rundunar sojin Bundeswehr ta nan Jamus, za ta ci gaba ne da girke wasu rukunanta a can.