1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan sauya fasalin MDD

Gazali Abdou Tasawa
September 18, 2017

A wannan Litinin din ce Shugaba Donald Trump na Amirka ke kaddamar da taron muhawar kan neman yi wa Majalisar Dinkin Duniya gyaran fuska da nufin shawo kan matsalar jinkiri wajen daukar muhimman matakai.

https://p.dw.com/p/2k9o9
New York UN Sicherheitsrat Nordkorea Sitzung
Hoto: Getty Images/AFP/K. Betancur

Kasashe 130 daya baya daya za su gabatar da jawabai inda za su bayyana matsayinsu da ma shawarwari a game da wannan bukata ta Shugaba Trump ta sauya fasalin tsarin aikin Majalisar Dinkin Duniya. A watan Agustan da ya gabata kasar Amirka wacce ke a sahun gaba wajen samar da kudaden gudanarwa ga Majalisar Dinkin Duniya ta nemi goyon bayan wasu kasashe 15 da suka hada da Faransa da Ingila da Jamus da Italiya wajen ganin sun ba ta hadin kai ga cimma wannan buri na yi wa Majalisar Dinkin Duniya gyaran fuska. A gobe Talata ne dai za a soma gabatar da manyan jawabai a babban taron koli na Majalisar inda batun rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa da kuma batun sauyin yanayi za su kasance a sahun gaban maudu'an da taron zai tattauna.