1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe yayi watsi da tayin Kungiyar Tariyar Afrika

Hauwa Abubakar AjejeAugust 18, 2005

Shugaban kasar Zimbabwe ya ce batun shiga tsakani bata taso ba a rikicin kasar

https://p.dw.com/p/BvaP
Shugaba Robert Mugabe
Shugaba Robert MugabeHoto: AP

Tsohon shugaban kasar Mozambique Joachim Chissano a karshen taron yankin kudancin Afrika, yace ba wani batun shiga tsakani a rikicin Zimbabwe, tunda a cewarsa daya daga cikin wadanda abin ya shafa wato shugaba Robert Mugabe yace batun hakan bata taso ba.

A makon daya gabata ne shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya kuma shugaban Kungiyar Taraiyar Afrika ya nada Chissano a matasayin mai shiga tsakani a rikici mafi muni na kasar Zimbabwe tun samun yancin kanta a 1980.

Kungiyar ta AU tayi fatar cewa daya daga cikin shugabanni da ake mutuntawa a yankin wato Chissano zai iya taka rawar gani na sasanta tsakanin jamiyar ZANU da ke mulki da kuma jamiyar adawa ta MDC,wadda take zargin jamiyar da mulkin da laifin yin aringizon kuriu don ta kasance bisa mulkin kasar.

Sai dai Chissano ya baiyanwa manema labarai cewa jamian gwamnatin Zimbabwe sun ce batun sasantawa bata ta so ba tunda a cewarsu wannan rikici ne na cikin gida kuma zasu iya magance shi da kansu.

Amma ita jamiyar MDC tayi maraba da wannan tayi na shiga tasakani tana mai cewa hakan zai taimaka share hanyar Mugabe dan shekaru 81 da haihuwa ya sauka daga mulki don a kafa gwamantain rikon kwarya wadda zata shirya babban zabe da zai bada damar kafa gwamantin hadin gwaiwa a kasar.

Shugaban jamiyar adawar Morgan Tsvangirai yayi gargadin cewa Chissano yana fuskantar babban kalubale na shawo kan Mugabe ya amince da wannan tayin na kungiyar AU.

Shi dai Mugabe ana shi bangare cewa yayi kasashen yamma suna anfani da jamiyar adawa ta MDC ne don su tunbuke shi daga karagar mulki.A makon jiya Mugabe yace ya fi anfani gareshi da ya tattauna da prime minister Tony Blair,wadda Mugaben yake ganin shine babban abokin adawarsa a kaashen yamma.

Jamiyara MDC ta karyata zargin tana mai cewa matsanancin halin da tattalin arzikin kasar ya shiga da karancin man fetur tare da hauhawar farashin kayayaiyaki,ya kamata su sanya shugaba Mugabe ya amince da a tattauna.

A wani rahoton kuma gwamnatin Zimbabwe ta zargi wakilin Majalisar Dinkin Duniya da son kai da kuma ko in kula da kokarin da Zimbabwen takeyi na samawa talakawan kasar mutunci da makoma mai kyau.

Wannan kalami dai yana kunshe ne wani martini mai shafuna 45 da gwamanatin Zimbabwen tayi game da Allah wadai da majalisar tayi mata akan rushe gidajen talakawa da tayi inda mutane kimanin dubu dari bakwai suka rasa gidajensu ko kuma aiyukansu.

Wannan shiri na Zimbabwe da tayiwa lakabi da “yakin kawar da tarkace”tace tayi ne da nufin magance dinbin matsaloli na tattalin arziki da yake da matukar illa ga rayuwar jamaar kasar.

Gwamnatin Zimbabwen tace Majalisar Dinkin Duniya tana kururuta yawan jamaa da tace Zimbabwen ta rusawa gidaje inda tace yawansu bai kai yadda MDD take cewa ba,hakazalika gwamnatin ta Zimbabwe tace zata ginawa wadannan mutane wasu sabbin gidajen.