1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe ya isa Lisbon

Zainab MohammedDecember 7, 2007
https://p.dw.com/p/CYnA

Shugaba Robert Mugabe na ƙasar Zimbabwe ya isa birnin Lisbon din ƙasar Portugal,domin halartan taron hadin gwiwa tsakanin kasashen turai da Afrika dazai gudana a karshen mako.A martanin sa dai prime minista Gordon Brown ,yayi barazanar kauracewa taron na yini biyu,dangane da sukan lamirin mulkin danniyya Britanian kewa gwamnatin Mugabe,na take hakkin jama’a.To sai sai shugaban majalisar Turai Hans-Gert Pöttering,yace abu mafi muhimmanci shine ganin ingantuwan dagantakaka tsakanin Afrika da turai.Kaza lika Shugaban kungiyar tarayyar turai Jose Manuel Barroso,yace taron nada nufin cimma hadin kai ta fannin tattalin arziki ,da muhalli tsakanin nahiyoyin biyu,waɗanda kuma sune mafi muhimmanci amma ba batun halartan kowane shugaba.